28 Yuni 2014 - 11:35
Mafi Yawan Kasashen Musulmi Gobe Lahadi Ne Za'a Fara Azumi

Mafi yawa daga cikin kasashen musulmi da na larabawa sun sanar da yau asabar a matsayin ranar karshe ta watan Sha’aban sannan kuma gobe Lahadi a matsayin ranar farko na watan Ramalana na wannan shekara ta 1435, duk da cewa wasu kasashen sun sanar da yau a matsayin ranar farko din.

Kasashen da suka sanar da gobe Lahadin a matsayin ranar farko na watan Ramalanan sun hada har da Saudiyya, Jordan, Kuwait, Bahrain, Masar, Siriya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa da sauransu.

A nan Iran ma dai a yau ne ake sa ran za a fara duban jaririn watan na Ramalana idan har ya tabbata to a gobe Lahadin ne za a fara azumin watan Ramalana. A wata sanarwa da ofishin Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar ya fitar ya ce tuni aka tura wani adadi mai yawa na masana da kayan aiki zuwa yankuna daban-daban na kasar don neman watan na Ramalana.

Tuni dai mahukunta a Nijeriya, ta bakin sarkin musulmi na kasar, Alhaji Sa’ad Abubakar, suka sanar da yau Asabar a matsayin ranar farko na watan Ramalana. A kasar Yemen ma mahukunta a kasar sun sanar da yau din a matsayin ranar farko na watan Ramalanan.ABNA